Dubban mutane ne suka hallara domin gudanar da Sallar Idi a fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa ta Nassarawa da ke Kano.
Sallar, wadda Sarkin Malamai Malam Kamalu Inuwa ya jagoranta, ta ba da wani yanayi na tunani da godiya ga Mahalicci.

A cikin hudubarsa, Malam Kamalu, ya gabatar da wani sako mai muhimmanci da jan hankali, inda ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su kiyaye dokoki da kuma rungumar dabi’un hakuri da juriya.

Haka kuma, ya jaddada yanayin rayuwar duniya ta wucin gadi, inda ya bukaci masu al’ummar musulmi da su dage wajen yin ayyukansu na alheri.












































