Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin tsare Omoyele Sowore, dan takar shugaban k asa na jam’iyyar AAC a Gidan Gyaran Hali na Kuje a ranar Litinin.
A wani kwarya-kwaryan hukunci, Mai Shari’a Mohammed Umar, ya bada umarnin a tsare Sowore a gidan gyara hali har sai an kammala sauraren karar kuma an yanke hukunci kan rokonsa na dakatar da umarnin soke belinsa da umarnin kama shi.
Mai Shari’a Umar ya kuma kori rokon farko da Sowore ya yi na neman mai shari’ar ya yi watsi da shari’ar bisa zargin nuna son zuciya.
Mai shari’ar ya dage shari’ar zuwa ranar 24 ga Yuni domin sauraron rokon dakatar da umarni.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa lauyan wanda ake kara, Adeyinka Olumide-Fusika SAN, ne ya shigar da rokon dakatar da umarni.
Tun da farko, NAN ta ruwaito da fari Sowore, wanda kuma shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters, ya isa kotun tare da mambobin kungiyarsa suna dauke da alluna.











































