PRP ta karyata zargin sayar da fom din ‘yan takara ga Kwankwaso

PRP logo gold (1)

Jam’iyyar PRP ta karyata zarge-zargen da ke cewa ta sayar da fom din takara na mutum 69 ga tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso domin kwace ikon jam’iyyar, tana mai cewa an riga an cike dukkan kujeru kuma Kwankwaso ba ma dan jam’iyyar ba ne.

Idan zaku iya tuna, Shugaban Kungiyar masu ruwa da tsaki na PRP shiyar Arewa maso Yamma, Abdulkadir Musa Giza, ya zargi Kwankwaso da sayen fom din Takara guda 69 a PRP don kwace tsarin jam’iyyar gabanin 2027.

Ya yi wannan zargin ne a wata ganawa da manema labarai ranar Lahadi.

Sai dai a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, Sakataren PRP Alhaji Musa Maigari ya ce ba a taba samun lamarin da Rabiu Kwankwaso ya sayi fom din takara na jam’iyyar ba.

“Yanzu haka an cike dukkan kujeru a PRP, an kammala zaben fidda gwani kuma kowace jam’iyyar siyasa ta kammala zaben fidda gwaninta,” in ji shi.

Maigari ya kara da cewa mutumin da ya yi zargin ba shi da alaka da PRP. “Mutumin da ya kawo wadannan zarge-zargen ba ma dan jam’iyyarmu ba ne. Abin dariya ne a wannan lokaci da aka riga aka kammala zaben fidda gwani , wani ya yi magana kan zaben fidda gwani ko fom din takara.”

Ya bayyana cewa irin wannan kungiyoyin babu su a cikin jam’iyyar PRP ma.

Sakataren ya dage cewa babu wata takarda ko bayani a sakatariyar jam’iyyar da ke nuna an yi ciniki ko sayar da fom ga Kwankwaso ko wakilan sa.

Maigari ya ce da’awar ta zo ne bama a lokacin da ya dace ba, ganin cewa PRP ta riga ta kammala zaben fidda gwaninta na zaben da ke tafe.

Ya roki jama’a da su yi watsa da jita-jita mara tushe”, kuma su dogara kadai da bayanai daga kafofin jam’iyyar a hukumance.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here