A daren ranar Talata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a gidansa, dake Abuja.
Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayani kan ganawar tasu ba, amma dai Tinubu ya ce ya kai ziyarar ta ban girma ne ga tsohon shugaban kasar a matsayinsa na daya daga cikin masu ruwa da tsaki a kasar nan.
Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC ya ci gaba da cewa ya kuma bayyana masa burinsa na zama shugaban kasa tare da neman goyon bayansa.
A yayin ziyarar Tunibu, ya samu rakiyar Dan takarar mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima da gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun sai Simon Lalong na jihar Filato da kuma Bello Matawalle gwamnan Zamfara, da sauransu.













































