An samu gawar wasu daliban Jami’ar Jihar Kwara biyu masu suna Malete Tobiloba Daniel, da wata da ake zargin budurwarsa ce Arewa Abayomi, a dakin Daniel dake wajen makaranta.
Rahotanni sun bayyana cewa dukkan mamatan daliban aji 2 ne na jami’ar kuma yanzu haka suna rubuta jarabawar karshen jangon karatu ne.
Yan uwansu Dalibai sun tabbatarwa manema labarai cewa a ranar Talata kimanin kwanaki uku kenan ba a gansu a wajen jarabawa ba.
Da take mayar da martani kan lamarin, Daraktar sashen yada labaran jami’ar, Dakta Saeedat Aliyu, ta ce kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan lamarin.
Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Kwara, SP Ajayi Okasanmi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an gano gawarwakin su, su biyu a cikin dakin Daniel, amma ana ci gaba da bincike da gano musabbabin mutuwarsu.













































