Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya amince da wasu muhimman nade-nade na gargajiya a majalisar masarautar Kano, bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.
SolaceBase ta ruwaito cewa Galadima Kano, Alhaji Abbas Sunusi ya rasu ne a ranar 1 ga Afrilu, bayan doguwar jinya.
Sarkin ya nada Alhaji Munir Sanusi a matsayin sabon Galadiman Kano, sarauta mai daraja da marigayi Abbas Sunusi ya rike.
Kafin hawansa, Munir Sanusi ya rike mukamin Wamban Kano kuma Hakimin Bichi.
Sarkin ya kuma daukaka darajar Alhaji Kabiru Tijjani Hashim zuwa Wambai, yayin da Mahmud Ado Bayero ya samu Turakin Kano.
Hakazalika Sarkin ya nada dansa Adam Lamido Sanusi wanda aka fi sani da Ashraf a matsayin sabon Tafidan Kano, yayin da Ahmed Abbas Sanusi dan marigayi Galadima aka nada Yariman Kano.
Wata majiya ta fadar ta tabbatar da nadin ga SolaceBase a ranar Talata, inda ta bayyana cewa hukuncin ya nuna yadda Sarkin ya jajirce wajen ci gaban al’adu, da nagarta da kuma kiyaye al’adun masarautar Kano.
Ana sa ran sabbin masu rike da mukaman da aka nada za su taka muhimmiyar rawa wajen bayar da shawarwari, jagoranci, da kokarin ci gaban al’umma a fadin jihar.