Sanata Mohammed Ali Ndume na jam’iyyar APC daga Borno ta Kudu ya yi kakkausar suka game da nade naɗen mukamai da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke yi, wanda a cewarsa, ya fifita wani bangare ko kabila, sabanin yadda dokokin tarayya suka tanada.
Ndume ya ce ya yi matukar kaduwa a lokacin da ya karanta jerin sunayen wadanda aka nada a siyasance na gwamnatin tarayya da ake yaduwa a kafafen sada zumunta, yana mai bayyana lamarin a matsayin wanda bai cika alkawarin sabunta tsare tsare kamar yadda ya bayyana lokacin da ya sha rantsuwar aiki.
Ndume ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Arise a ranar Litinin.
Ya yi nuni da cewa a matsayinsa na dan majalisa, kuma bisa lura da ya yi, nade-naden da Shugaba Tinubu ya yi ya zuwa yanzu sun saba wa tsarin tarayya, don haka ya kamata a gyara su.
Sanatan wanda dan jam’iyyar APC mai mulki ne, ya kasance mai yin kakkausar murya da suka, musamman a kan wasu tsare-tsare na gwamnati da yake zargin ba sa cikin muradun talakawan Najeriya da masu zabe.
Da yake amsa tambaya kan jerin sunayen mutanen da shugaban kasa ya nada a siyasance, wanda ake yadawa kuma suka nuna ana goyon bayan wata kabila, Ndume ya ce, “To, ba na jin ba ni da wani abu da zan karawa, domin alkaluman suna nan, za ku iya dubawa, ba wai ina zarge-zarge ne ko na ce shugaban kasa ba shi da hurumin yin nade-nade a cikin kundin tsarin mulkin kasa ba, sai dai nadin da aka yi zuwa yanzu, nadi ne na siyasa.