Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Marigayi Ummaru Yar’Adua

‘Ba za mu taɓa mantawa da kai ba’ – Tinubu

A yau, kamar kullum, ina tunawa da abokina kuma dan uwana na kwarai a fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da shugabanci nagari a Najeriya, marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua, wanda ya rasu a rana irin ta yau shekaru 13 da suka gabata.

5 Ga watan Mayu, 2010, ga wasunmu ga wasun mu har yanzu abin sabo ne. Muna tunawa da ranar kamar yadda muke tunawa da rayuwa mai ma’ana da Mallam Umaru Yar’Adua ya yi.

A matsayinsa na abokina kuma dan siyasa ina mutunta abubuwan da suka faru na gaskiya, dagewa, kishin kasa da nagartar aikin gwamnati wanda Marigayi ‘Yar’adua ya bari a baya a matsayin gwamnan jihar Katsina (1999 zuwa 2007) da shugaban Najeriya (2007 zuwa 2010). .

A yayin da nake shirin karbar ragamar shugabancin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu, na kuduri aniyar yin koyi da kyawawan misalai da shugabanni irin su Malam Umaru ‘Yar’adua suka bayar da suka baje kolin nagarta da sadaukar da kai ga kasarmu.

Ka huta cikin farin ciki dan uwana. Da fatan ranka ya ci gaba da samun kyakkkyawar makoma gurin Mahaliccinka, ameen.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Zababben shugaban kasar tarayyar Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here