Magoya bayan gwamna Wike sun zare jikin su daga cikin wadan da zasu jagoranci gangamin yakin neman zabe Atiku Abubakar.
Magoya bayan sun ce ba wata alaka tsakanin Wike da Atiku har sai shugaban jam’iyyar, Ayu ya sauka daga mukamin sa, ya kuma bada kujerar sa ga wani daga kudu ya jagoranci jam’iyyar.
Hakan na dauke cikin wata takardar cemma matsaya, wacce suka rabawa manema labarai bayan kammala taro da aka shafe na tsawon awa bakawai, da magoya bayan Wike suka gudanar a gidan gwamnatin jihar na musamman dake Port Harcourt yau Laraba.
A cikin takardar da tsohon gwamnan jihar Ogun, a zamanin milkin soja, Bode George ya karanta, ya ce dole ne shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu, ya sauka daga kujerasa ya bawa ‘yan Kudu dama.
Takardar ta kara da cewa ba wai suna goyan bayan Wike Bane sabo da ya fade a zaben fitar da gwani, ko kuma don anki daukar sa a matsayin mataikin shugaban kasa, suna mara masa baya ne domin tabbatar da adalci a jam’iyyar su ta PDP.
Wadan da suka halarci taron sun hada da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, Ayo Fayose Ekiti, Donald Duke Cross River, Ibrahim Dankwambo Gombe, Jonah Jang Plateau, da kuma tsohon babban lauyan Najeriya, Mohammed Adoke.
Sauran sun hada da erry Gana, shugaban jam’iyyar PDP shiyar Kudu masu Kudu, tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilan Najeriya, Chibudom Nwuche, Suleiman Nazif, Nnenna Ukeje, da sauran su.










































