Peter Obi ya gana da magoya bayansa a Canada

FB IMG 16617783223304682
FB IMG 16617783223304682

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Naeriya, ƙarƙashin Jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi ya gana da magoya bayansa da ke zaune a ƙasar Canada.

Mista Obi ya yi jawabi a taron da aka yi wa taken “Kyakykyawan tasirin da mazauna ƙasashen waje za su yi ga ci gaban Najeriya”.

A cikin jawabin da ya yi, Mista Obi ya faɗa wa taron dalilan da suka sa ya tsaya takarar Shugaban Najeriya.

Ƴan Najeriya mazauna Canada ne dai suka shirya taron a wani ɓangare na gano rawar da za su taka ga haɓakar Najeriya

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here