Zargin cin Hancin Biliyan 2.2: Kotu ta tsare Ngige a gidan yari,har sai ya cika sharadin beli

Dr Chris Ngige 750x430

Kotun babban birnin tarayya ta Abuja ta umarci a ajiye tsohon ministan ayyuka da samar da aikin yi Chris Ngige a gidan gyaran hali na Kuje, domin jiran lokacin da za a saurari bukatar belin da lauyansa zai gabatar.

Hukumar yaƙi da cin hanci da laifukan tattalin arziki ta tuntubi kotu da tuhumar cewa Ngige ya karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai Naira Biliyan 2.2 lokacin da yake rike da kujerar ministan ayyukan yi, tare da wasu laifuka da suka shafi karɓar rashawa da cin gajiyar mukami.

Rahoton ya bayyana cewa Ngige, wanda ya taɓa zama gwamnan Anambra a karkashin jam’iyyar PDP, yana fuskantar tuhume-tuhume da suka haɗa da bayar da kwangiloli ga kamfanonin abokan aikinsa ta hannun Hukumar Inshorar Jama’a ta Najeriya, waɗanda jimillar kudinsu ta kai miliyoyin Naira.

Hukumar ta zargi cewa kamfanonin da ake danganta da abokan Ngige sun ci gajiyar kwangilolin da suka shafi horo, kayan aiki da kuma aikin ba da shawara, lamarin da ya sabawa sashen 19 na dokar yaƙi da cin hanci da rashawa na shekara ta 2000.

Karanta: Kotun koli ta sake tabbatar da hukuncin kisa ga Maryam Sanda, ta soke afuwar da Tinubu ya yi mata

Hukumar ta kuma gabatar da bayanai kan kudaden da Ngige ya karɓa ta wata kungiya tasa, inda ta ce hakan ya sabawa dokar hana jami’an gwamnati karɓar wani nau’i na alheri daga kamfanonin da suke hulɗa da gwamnati, duk da cewa lauyansa ya nemi a ba shi beli bisa dalilin rashin koshin lafiya.

A zaman shari’ar, kotu ta ce ba za a bayar da beli ba saboda babu cikakken bayani kan takardun sharudan belin da ake bukata, musamman batun fasfo ɗinsa da lauyansa ya ce an sace, alhali hukumar yaƙi da cin hanci da laifukan tattalin arziki ta ce ba ta samu wata sanarwa ba.

Mai shari’a Maryam Hassan ta dage zaman zuwa ranar Litinin domin sauraron bukatar belin, tare da bayyana cewa nan ne za a tantance ko za a bada belin ko akasin haka.

NAN.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here