Kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 26 ga Fabrairu, 2026 domin yanke hukunci a shari’ar da Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta shigar kan DCP Abba Kyari da ‘yan uwansa biyu game da zargin boye kadarori da rashawa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa hukumar tana tuhumar tsohon shugaban rundunar bincike ta musamman ta ‘yan sanda tare da ‘yan uwansa bisa tuhumar kin bayyana kadarorinsu yadda doka ta tanada.
Wannan ya biyo bayan bayanan da lauyoyi na bangarorin biyu suka gabatar bayan kammala muhawara kan tuhume-tuhumen.
Hukumar ta gabatar da tuhumar da ta ƙunshi jerin kadarori 14 da ta ce an gano sun kasance mallakar Kyari, ciki har da shagunan kasuwanci, gidajen zama, filayen wasanni, gonaki da ƙasa a wurare daban-daban na babban birnin tarayya Abuja da Maiduguri a Borno, tare da wasu adadi na kudi da aka gano a asusun ajiyarsa a bankuna daban-daban.
A cewar hukumar, ta kuma gano fiye da Naira Miliyan 207 da Euro 17,598 a cikin wasu asusun ajiyar Kyari, sannan ta zarge shi da boye mallakar kadarori da kuma karkatar da wasu kuɗaɗe, abin da ya sabawa sashe na 35(3)(a) na dokar NDLEA da sashe na 15(3)(a) na dokar hana wadaƙa da kuɗi ta 2011.
Bayan rufe gabatar da shaidu, Kyari ya nemi kotu ta wanke shi kai tsaye bisa cewa ba a gabatar da sahihan hujjoji da ke tabbatar da cewa kadarorin nasa ba ne, sai dai kotun ta yi hukunci cewa akwai dalilai da suka isa a ci gaba da shari’ar, don haka ya buƙaci gabatar da kariya.
Karanta: Zargin cin Hancin Biliyan 2.2: Kotu ta tsare Ngige a gidan yari,har sai ya cika sharadin beli
Ya bayyana cewa, tunj ya bayyana kadarorinsa bisa doka, kuma wasu daga cikin kadarorin da aka ambata mallakin mahaifinsa ne wanda ya bar ‘ya’ya da dama.
Kyari ya musanta mallakar filin wasan polo da aka danganta shi da shi, sannan ya kammala kare kansa bayan an yi masa tambayoyi a kotu.
Amma ‘yan uwansa biyu sun sanar da kotu cewa ba za su kira wani shaida ba, kuma za su dogara da bayanan da hukumar NDLEA ta gabatar.
Wannan shari’ar ta bambanta da ta fataucin Koken da hukumar ta gurfanar da shi tare da wasu jami’an ‘yan sanda a wata kotun tarayya daban a Abuja.
Duk dai shari’o’in biyu an shigar da su ne a shekarar 2022.













































