Shugaban Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano, Lawan Najume Kabo, ya kore Sakataren mulki tare da wasu masu rike da mukaman siyasa guda hudu bisa zargin kasancewarsu mambobin kungiyar goyon bayan Tinubu Maliya Shonikan (TMS) a Jihar Kano.
SolaceBase ta ruwaito cewa an tsige wadannan jami’ai ne a lokacin wani taron gaggawa da Shugaban Karamar Hukumar Kabo ya jagoranta a yammacin ranar Talata.
Wadanda lamarin ya shafa sun hada da Abba Salisu Mewake Garo Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Kabo, Kansila mai gafaka, Ahmad Yusuf Chiroma Godiya, Mashawarci a bangaren ilimi, Hon. Tanimu Garba Garo da Mashawarci a bangaren harkokin addini, Yakubu Sa’adu Gammo.
An danganta daukar wannan mataki da shigar wadannan jami’ai cikin kungiyar (TMS), wata kungiya da ke tallata muradun siyasar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin a Jihar Kano.
Bayan korarsu, Shugaba Lawan Najume ya rantsar da wasu sabbin mutane domin maye gurbinsu, don cika guraben da suka bari nan take.













































