Wani sashe na kotun kolin ya ci wuta a safiyar ranar Litinin, duk da cewa ba a sami asarar rai ba.
Jami’in hulda da jama’a na kotun, Mista Festus Akande, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce musabbabin gobarar wutar lantarki ce daga daya daga cikin canbobin alkalai kuma an kashe wutar da na’urorin kashe gobara na kotun nan take.
Akande ya kara da cewa labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta na cewa an samu asarar rayuka “labari ne na karya”.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safe.