Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya kwace filaye guda 21 a babban birnin tarayya (CBD) da ke Abuja.
A cikin sanarwar janyewar da Mista Olusade Adesola, babban sakatare a hukumar babban birnin tarayya Abuja ya sanya wa hannu a madadinsa, Wike ya bayyana cewa an soke filayen ne saboda saba doka da sukai.













































