Al Jazeera a ranar Lahadi ta ce kasar Sudan ta soke lasisin Al Jazeera Mubasher, wani bangare na cibiyar sadarwa da ke Qatar wanda ke gudanar da shiri kai tsaye.
Hukumomin kasar sun zargi da nuna “rashin kwarewa wajen watsa shirye-shiryen game da zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji da aka gudanar a kasar.
“Hukumomin Sudan sun sanar da soke amincewar Al Jazeera Mubasher tare da hana tawagarta yin aiki a Sudan,” in ji Al Jazeera a wani sako da ta wallafa a twitter.
Sudan dai ta fada cikin rudanin siyasa tun bayan da babban hafsan sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kaddamar da juyin mulki a ranar 25 ga watan Oktoba.
Juyin mulkin da sojoji suka yi ya janyo zanga-zangar neman mulkin farar hula. Sojoji sun mayar da martani da kakkausar murya.
Akalla masu zanga-zangar 64 ne aka kashe, a cewar masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya, kuma wani dan sanda shi ma ya rasa ransa.
Al Jazeera ta ba da fitattun labarai game da zanga-zangar kuma a karshen shekarar da ta gabata ma ta watsa wata hira da Burhan.
A watan Nuwamba, kwanaki bayan tattaunawar, ta ce an kama shugaban ofishinta na Khartoum Al-Musalami Al-Kabbashi a gidansa.
Babban editan jaridar sojojin kasar Ibrahim al-Hory daga baya ya zargi Kabbashi da buga bayanan “karya” da kuma yada “tsoffin faifan bidiyo wadanda suka haifar da rikici” a kasar.













































