Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, a ranar Lahadin da ta gabata, ya shaida wa Majalisar Dokoki ta kasa cewa yin watsi da matsayar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kudirin gyaran dokar zabe ba shi ne zabi mafi kyau ba.
Jega ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wajen wani taro kan kudirin dokar zabe na 2021, wanda Yiaga Africa da abokan hulda suka shirya.
A cewarsa, kasar za ta yi kyau idan ta shiga zabe mai zuwa da sabuwar dokar zabe domin hakan zai kara inganta nagarta da kuma shirye-shiryen gudanar da zabe.
Ya ce kudurin dokar ya kunshi abubuwa masu kyau da yawa wadanda za su iya inganta sahihancin tsarin zabe baya ga batutuwan da suka shafi zaben fidda gwanin kai tsaye domin Najeriya ba ta samu wani ci gaba mai ma’ana ba kan dokar zabe tun daga shekarar 2010.
“A kan zaben fidda gwanin kai tsaye, a fili tsarin zabe zai fi samun ingantacciyar gaskiya idan muka yi zaben fidda gwani kai tsaye yadda ya kamata, ‘yan majalisar dokokin kasa sun san cewa gwamnoni suna murde zaben fidda gwani na kai tsaye kuma suna tunanin cewa idan suka shiga zaben fidda gwanin kai tsaye za su iya ‘yantar da kansu daga hakan irin magudi.
“Duk da haka, muna bukatar mu yi wa wannan al’amari tambayoyi da kyau, don haka shawarata ita ce a bai wa INEC doka ta fara shirye-shiryen tunkarar zaben 2023.
Jega ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da ta yi abin da ake bukata maimakon tsayawa cece-kuce kan matsayar Shugaban kasa.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a nasa jawabin, ya ce gwamnonin jihohi 36 ba sa tsoron zaben fidda gwanin kai tsaye kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke zarginsu.
Sule, ya ce abin da suke adawa da shi, hanya ce da za ta iya takaita zabin mutane.
“A kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC, muna da zabi guda uku: yarjejeniya, zaben fidda gwani kai tsaye da wanda ba kai tsaye.
“Ya kamata a bar zabin a bude kuma ba zai zama abin mamaki ba cewa wasu jam’iyyun na iya yin zaben fidda gwani kai tsaye.
“Gwamnoni sun ji dadin irin gudunmawar da aka bayar a cikin kudirin kuma daga abin da na ji kowa na fadin haka ne, don haka a cire batun zaben fidda gwanin kai tsaye.
“Ni ba na kusa da shugaban kasa bane amma ina aiki da shugaban kasa duk lokacin, zan iya cewa shugaba Buhari zai sanya hannu kan kudirin dokar da zarar an yi abubuwan da suka dace,” inji shi.
Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Olumide Akpata, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda al’amura suka kasance a kan kudirin.
Akpata ya ce komai game da kudirin zaben ya nuna an samu ci gaba amma ana bukatar daukar matakan da suka dace domin samun daidaito ta hanyar tunani kafin aiwatar da shi.
Ya shawarci Majalisar Dokoki ta kasa da ta fitar da tanade-tanaden zaben fidda gwanin kai tsaye tare da mika kudirin ga shugaban kasa nan take domin amincewa.
Babban Daraktan Yiaga Africa, Samson Itodo, ya ce Najeriya na da kimanin kwanaki 399 kafin zaben shekarar 2023 kuma amincewa da kudirin a kan lokaci zai kasance da amfani wajen zurfafa dimokaradiyya da ci gaban kasa.
Itodo ya ce wani abin da bai wuce haka ba zai sawa ‘yan Najeriya damar aiwatar da muhimman abubuwan kirkire-kirkire a zaben kananan hukumomin babban birnin tarayya Abuja da kuma zaben gwamna a jihohin Ekiti da Osun.
A nata bangaren, Jakadiyar Kungiyar Tarayyar Turai a Najeriya da kungiyar ECOWAS, Samuela Isopi, ta ce yana da kyau a samu ci gaban dimokuradiyya a daidaita dokokin zabe.
A nata bangaren, wata tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasa, jam’iyyar KOWA, Farfesa Remi Sonaiya, ita ma ta yi kira da a cire maganar zaben fidda gwanin kai tsaye, tunda wannan ita ce matsalar domin a zartar da kudirin.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Mista Ayuba Wabba, ya ce lokaci ya kure, don haka dole ne Majalisar Dokoki ta cire wasu kujerun da ke damun dokar zabe, sannan ta shirya komai kafin zaben 2023.
Ya yi mamakin dalilin da ya sa Najeriya ba ta sa hannu kan kudurin ECOWAS da Tarayyar Afirka (AU) na cewa a shirya dokar zabe shekara guda kafin zabe.
Dan majalisar wakilai, Hon. Dachung Bagus, ya ce masu ba da shawara da aka ba kwangilar aikin ne ke da alhakin wasu kura-kurai da aka yi a cikin kudirin.
“Muna neman afuwar kurakuran da aka yi da kuma gibin da aka samu a cikin Kudirin Zabe na 2021,” in ji shi.










































