Naira miliyan 300 da jihar Rivers ta ba mu kyauta ne, ba kudin karbar bakuncin taro ba – NBA ta yi martani ga Ibas

NBA NBA

Kungiyar lauyoyin Najeriya NBA ta yi karin haske kan cewa Naira miliyan 300 da ta karba daga hannun gwamnatin jihar Rivers kyauta ce da ba za a iya mayarwa ba, ba wai ta biya hakkin daukar nauyin babban taronta na shekara-shekara ba.

A baya dai kungiyar ta NBA ta mayar da taron da ke tafe zuwa jihar Enugu bayan ayyana dokar ta baci a Rivers.

A martanin da gwamnatin jihar Ribas ta yi a ranar Litinin din da ta gabata, ta bukaci a maido da makudan kudin har miliyan 300.

Labari mai alaƙa: Ku dawowa da Jihar Rivers Naira miliyan 300 na karbar bakuncin babban taron shekara -Ibas ya fadawa NBA

NBA, a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin tsare-tsare na AGC 2025, Emeka Obegolu SAN ya fitar, ya ce: “An jawo hankalin kwamatin tsare-tsare na babban taron shekara-shekara kan wata sanarwa da mai kula da jihar Rivers ya fitar kan yadda gwamnatin jihar ta biya hakkin karbar bakuncin NBA na 2025.

Idan ba a manta ba, a ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyar NBA ta bayyana cewa, matakin da babban jami’in gwamnatin jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) ya yi, ya gurgunta cibiyoyi da tsarin dimokuradiyya.

A cewar NBA, Ibas yana gudanar da aiki ba tare da la’akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma kararrakin da ake ci gaba da yi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here