NFF ta musanta cewar tanabin Christian Chukwe kudi bayan rasuwar sa

Christian Chukwu

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta yi watsi da rahotonnin da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa kungiyar na bin tsohon kyaftin din kungiyar Super Eagles kuma mai horarwarta, Christian Chukwu kudi.

A ranar Asabar 12/4/2025 ne dai Chukwu ya rasu sakamakon rashin Lafiya.

Rahotonnnin dake yawo na zargin cewa hukumar kwallon kafar ta kasa NPP na bin Chukwu bashin dalar Amurka 128,000.

Labari mai alaƙa: Tsohon mai horar da kungiyar Super Eagles Christian Chukwu ya rasu yana da shekaru 74

Gidan Jaridar FIJ dai ya rawaito cewa a shekarar 2008 Chukwu ya bayyana cewar hukumar ta NFF na binsa bashin dala 128,000, kuma ya yi ikirarin haka a wata hira da ya yi da The Athletic Nigeria, wata jaridar internet ta labaran wasanni, a watan Afrilun 2024.

Shekaru da yawa, babu wata shaida a bainar jama’a game da hukumar kwallon kafa ta kasa musamman ta musanta ikirarin Chukwu.

Sai dai a wani martani da ya mayar, babban sakataren hukumar ta NFF, Dakta Mohammed Sanusi, ya karyata wannan ikirari, inda ya tabbatar da cewa babu wannan batu a cikin takardun hukumar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here