Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya ta SSANU da ke cikin Jami’ar Bayero a Kano ta gargadi cewa za ta iya shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani idan gwamnatin tarayya ta kasa magance batutuwan da suka daɗe suna fuskantar jinkiri tun yarjejeniyar shekarar 2009 da sauran korafe-korafe da ƙungiyar ta gabatar.
Shugaban ƙungiyar Mustapha Aminu ya bayyana wannan matsayi a lokacin ganawa da ‘yan jarida a ranar Alhamis yana mai nuna cewa matakin ya biyo bayan umarnin da babban ofishin ƙungiyar na ƙasa ya bayar.
Ya bukaci gwamnatin tarayya ta gayyaci ƙungiyar domin ci gaba da tattaunawa don guje wa yajin aikin da ke gabatowa yana mai jaddada cewa muhimman matsaloli da dama sun daɗe ba a warware su ba a cikin tsarin jami’o’i.
Ya bayyana wasu daga cikin korafe-korafen ƙungiyar ciki da batun rashin aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar shekarar 2009 da kuma al’amuran da suka shafi kudaden ƙarin aiki da abin da ya kira rabon kuɗaɗen da bai yi daidai ba tsakanin ƙungiyoyin jami’o’i.
Karanta: A karon farko Gwamna Kano ya amince da naɗin mace a matsayin shugabar jami’ar Northwest Kano
Ya tunatar da cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin sakin kuɗin alawu amma daga baya aka ware kaso arba’in cikin ɗari ga wata ƙungiya guda kuma aka bar sauran Naira Biliyan Goma ga sauran ƙungiyoyi uku wanda ya bayyana a matsayin rabon da bai dace b
Ya kuma bayyana cewa ko da akwai ƙarin albashi da aka amince da shi shekaru biyu da suka gabata gwamnati ta gaza haɗa dukkan ƙungiyoyin da abin ya shafa a cikin tattaunawar da aka shirya domin sabunta tsarin, ciki har da ƙungiyoyin NAT, NASU da ASUU.
Ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar SSANU ta shirya tsaf domin shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani da zarar babban ofishin ƙungiyar ya bayar da umarni, ba yana masu cewa ba za a koma baya ba idan an bayar da umarnin fara yajin aikin.









































