Gwamnatin jihar Katsina za ta fara binciken badakalar daukar malaman firamare dubu 7 da 325 da aka yi a kwanakin baya.
Kwamishiniyar harkokin mata Hajiya Zainab Musa-Musawa ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Katsina bayan taron majalisar zartarwa ta jihar a ranar Laraba.
A kwanakin baya gwamnatin jihar ta dauki malamai sama da dubu 7 da suka yi nasara bayan zana jarabawar daukar aiki.
Kwamishiniyar ta ce gwamnati ta yanke shawarar yin bincike kan lamarin ne bayan samun korafe-korafe kan yadda aka gudanar da daukar aikin.
Ta kuma bada tabbacin cewa gwamnati za ta dauki mummunan mataki akan wadanda ke da hannu a badakalar daukar malaman.
Karanta Kari:Jami’ar Bayero ta kori dalibai 27 kan zargin satar jarrabawa
A nasa bangaren, Kwamishinan Kudi, Alhaji Bishir Tanimu, ya ce gwamnati za ta fara aiki da shirin asusun bai daya ga ma’aikatu da hukumomin jihar daga watan Janairun 2024.
A cewarsa, shirin zai tabbatar da sarrafa dukkan kudaden da ke shiga cikin asusun gwamnatin jihar, ta yadda za a toshe hanyoyin badakala.