Jami’ar Bayero ta kori dalibai 27 kan zargin satar jarrabawa

BUK 1 2
BUK 1 2

Jami’ar Bayero a Kano, ta yi karin haske kan dalilanta na korar dalibai 27 bisa zarginsu da satar jarabawa.

Jami’ar ta Bayero ta ce na dauki matakin koarar daliban ne bayan zaman da majalisar malaman jami’ar ta gudanar a ranar 26 ga watan jiya na Janeru.

Haka-zalika jami’ar ta ce akwai wasu ɗaliban da zasu sake maimita shekarar ɗaya, sannan ta ja kunnen wasu sama da 20.

Jami’in hulɗa da jama’a na Jami’ar ta Bayero, Lamara Garba, ya yi wa Khalifa Shehu Dokaji ƙarin bayani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here