Ganduje Ya Nada Babban Mataimaki Na Musamman A Fannin Sanya Ido Da Bunkasa Ayyuka

Farouq Sule Garo
Farouq Sule Garo

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Hon. Farouq Sule Garo a matsayin Babban Mataimaki na Musamman kan Sanya Ido da Bunkasa Ayyuka.

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren bincike, sanya ido da harkokin siyasa na ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota.

Karanta Wannan:Fursunoni Sama da Ɗari Biyu Sun Tsere a Jihar Kogi

Sanarwar tace, ”An nada ka a wannan matsayin ne bayan amincewa da rikon amanarka da ƙwarewa bisa cancanta, sadaukar da kai ga aiki, kishin ƙasa da gaskiya. Ana fatan za ka ci gaba da amfani da waɗannan kyawawan halayen naka wajen sauke nauyin da aka dora maka.

Hon. Farouq Sule Garo yana da Digiri na farko daga Jami’ar Hertfordshire a Ƙasar Ingila a fannin Tattalin Arzikin Kasuwanci, ya kuma yi digiri na biyu daga wannan jami’ar a fannin kula da Kudade.

Karanta Wannan: {BIDIYO}:Yadda Aka Ceto Ɗalibai 75 Da Aka yi Garkuwa Da Su A Zamfara

Kafin nadin nasa, shi ne Mamallakin kamfanin F.S. Garo International Limited. Dake harkar Man Fetur da Gas, da kuma Gidaje, da harkar Sufuri da sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here