{BIDIYO}:Yadda Aka Ceto Ɗalibai 75 Da Aka yi Garkuwa Da Su A Zamfara

Zamfara abductees new
Zamfara abductees new

Dalibai 75 na Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya, da ke Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara da aka sace a ranar 1 ga Satumba, 2021, sun kuɓuta daga hannun yan bindiga.

A cikin wani faifan bidiyo biyu da jaridar Solacebase ta samu, an ga Gwamna Bello Matawalle yana magana da wasu daga cikin daliban mata da aka ceto, inda yake tambayar su halin da suke ciki a hannun ‘yan bindigar.

Wata majiya ta shaidawa Solacebase cewa an ceto yaran ne da yammacin Lahadi.

Ko da yake bai fadi yadda aka kubutar da su ba, ko dai ta hanyar biyan kudin fansa ko ta hanyar shiga tsakani.

Karanata Wannan: Hukumar ICPC Za ta Gurfanar Da ‘Yan Kwangilar Da Suka Yi Ha’inci Wajen Gudanar Da Ayyukan Mazabu A Kano

Idan za a iya tunawa Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayar da rahoton cewa‘ yan bindiga sun sace dalibai sama da 70 a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here