PDP za ta ruguje a karshen 2025, don haka ka koma APC yanzu – Ganduje ga Lamido

imgonline com ua twotoone nLjTzIZ84yAaO 750x430

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya karyata rahotannin da ke nuni da cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP, inda ya kara jaddada goyon bayan sa ga jam’iyya mai mulki.

Ganduje, wanda ke mayar da martani ga wani tsokaci da aka danganta ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, na cewa nan ba da jimawa ba jam’iyyar APC za ta wargaje, kuma wadanda a baya suka bar PDP ciki har da tsohon gwamnan jihar Kano za su koma jam’iyyar adawa, ya ce maimakon shi ya koma PDP, nan ba da jimawa ba APC za ta karbi jigon PDP a cikinta.

Da yake magana ta bakin babban sakataren yada labaran sa, Edwin Olofu a Abuja, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana wannan ikirarin a matsayin mara tushe kuma rashin hankali, yana mai jaddada cewa babu dalilin da zai sa shi ficewa daga jam’iyya mai mulki saboda abin da ya bayyana a matsayin ‘yan adawa da suka gaza.

Ganduje ya yi hasashen cewa jam’iyyar PDP za ta ruguje a karshen shekarar 2025, bisa rigingimun cikin gida a jam’iyyar.

Karin karatu: Bukola Saraki zai jagoranci kwamitin sulhu na PDP

“A bayyane yake ga duk mai hankali cewa a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, jam’iyyar APC na ci gaba da samun tagomashi, inda manyan ‘yan siyasa a fadin kasar nan ke sauya sheka zuwa jam’iyyar da yawan gaske.

“Tare da irin wannan gagarumin goyon bayan na kasa, jam’iyyar APC ta ci gaba da mayar da hankali wajen karfafa nasarorin da ta samu da kuma shirya gagarumin nasara a zaben 2027. A gaskiya nan ba da dadewa ba za mu karbi Sule Lamido saboda nan ba da dadewa ba zai samu inda zai je, domin PDP ta mutu,” in ji Ganduje.

Ganduje ya jaddada alfaharinsa na shugabancin jam’iyyar APC tare da jaddada aniyarsa na zurfafa dimokuradiyyar jam’iyyar cikin gida da kuma samar da dorewar shugabanci da ci gaba.

Ya shawarci Lamido da ya maida hankali wajen magance rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP maimakon shiga cece-kuce marasa tushe.

Ganduje ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa jam’iyyar APC ta ci gaba da kasancewa a dunkule, ta mai da hankali, da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukanta ga al’ummar Nijeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here