Bayo Onanuga, Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Tinubu a Bangaren Yada Labarai da Dabarun Sadarwa, ya ce da yawa daga cikin ’yan Najeriya na amfana da manufofin sauye-sauyen tattalin arziki na gwamnatin yanzu.
Onanuga ya bayyana haka ne a shirin Prime Time na tashar Arise a ranar Talata, inda ya kare manufofin shugaban kasa ya kuma musanta ikirarin cewa akwai wahala da rashin tsaro baki daya a fadin kasar.
Ya kuma ce an karfafa ra’ayin cewa akwai yunwa baki daya ne sakamakon labaran da suka yadu tun da Tinubu ya hau mulki.
“An kulle mu cikin zato da hukunce-hukunce,” in ji shi.
“A farkon wannan gwamnati, wani ya saki wata murya yana cewa muna fama da yunwa. Tun daga lokacin, mutane suka cigaba da cewa haka.”
“Ni ’dan Najeriya ne, ina da mutane da ke yi min aiki a gida. Ba na ganin yunwar da mutane ke cewa akwai, domin ina ganin su ma’aikatan, ina ci gaba da yi musu tambaya. Ya rayuwa? Ya suke daidaita kansu? Wadanne matsaloli suke fuskanta?”
Onanuga ya ce ’yan Najeriya sun fara fahimtar tasirin ayyukan more rayuwa da gwamnatin tarayya ke yi a fadin kasar.
Ya ba da misali da abin da ya faru yayin da yake tafiya daga Ibadan zuwa Legas, yana mai cewa ya yi mamaki ganin wata sabuwar hanya ta kankare da ta ratsa ta Ijebu-Ode.
“Wata rana na yi tafiya daga Ibadan zuwa Legas, sai Google Maps ta ce min akwai cunkoso yayin da na kusa da Legas. Sai na yanke shawarar bi ta Ijebu-Ode ta Sagamu. Abin da ya burge ni shi ne na ga na tsinci kaina a kan wata hanya ta kankare. Na ce, ‘Kai, menene wannan, yaushe aka gina ta?’” in ji shi.
Ya kuma ambaci Asusun Ba da Lamuni ga Daliban Najeriya na NELFUND da na Lamuni ga Masu Amfani da CreditCorp a matsayin shirye-shiryen da ke ba ’yan kasa dama kai tsaye.
Onanuga ya kuma zargi kafafen yada labarai da yin abin da ya wuce kima wajen ruwaito kalubalen tsaron kasar, yana cewa rahotanninsu kan ba da ra’ayin cewa duka kasar ba ta da tsaro.
“Kafafen yada labarai a Najeriya su ne suke kirkirar matsala, yadda suke ruwaito rashin tsaro yana nuna cewa dukan kasar ta tsinci kanta cikin rikici,” in ji shi.
Onanuga ya kuma musanta maganganun da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC ya yi a kwanakin baya kan wutar lantarki.
Onanuga ya zargi Obi da rashin sanin yawan megawatt din da Najeriya za ta iya samarwa.
Ya kara da cewa babbar matsalar da ke fuskantar fannin wutar lantarki ita ce rashin iskar gas, wanda ya danganta da basussuka na sama da tiriliyan 4 da kamfanonin wuta ke bin kamfanonin gas.













































