Tsohon Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa wasu daga cikin alkalan da suke sauraren shari’ar zabe suna siyar da hukunci ga dan takarar da yafi basu kudi, daga bisani kuma su yi ritaya domin kaucewa hukunci daga hukumar kula da alkalai ta kasa.
Farfesa Jega wanda tsohon Shugaban jami’ar Bayero dake Kano ne, ya bayyana hakan ne yayin gabatar da muqala a wajen daya daga cikin tarukan makon lauyoyi, wanda kungiyar lauyoyi ta kasa reshen Ibadan ta shirya.
Ya ce da yawa daga cikin manyan lauyoyi sun zama masu arziki ta hanyar karbar makudan kudi daga wajen ‘yan ‘yan siyasa domin samar min musu nasara a gaban kotu.
A cewar Farfesa Jega lalacewar bata tsaya ga lauyoyi Kawai ba, har ta kai ga alkalai masu yanke hukunci da ya shafi yan siyasa. Inda yace yanzu harkar shari’a ta zama iya kudin ka iya shagalin ka, wanda ya bayar da kudi masu yawa shine yake yin nasara.
Ya ce akwai bukatar kungiyar lauyoyi ta kasa NBA da sauran kungiyoyin shari’a su dauki mataki domin shawo kan wannan matsala wadda ke daya daga cikin matsalolin dake kawo Shugabannin da basu cancanta ba, wanda ke janyo koma baya ta fuskar ci gaban kasar.










































