Uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu ta isa Kano

Remi Tinubu, kano, uwargidan,
A ranar Litinin ne uwargidan shugaban kasar Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta kai ziyararta na farko a jihar Kano. Jirgin shugaban kasa wanda ke kai...

A ranar Litinin ne uwargidan shugaban kasar Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta kai ziyararta na farko a jihar Kano.

Jirgin shugaban kasa wanda ke kai uwargidan shugaban kasa da tawagarta sun isa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalin karfe 10:15 na safe, wanda gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ‘yan majalisar ministocinsa da dubban magoya bayan jam’iyyar NNPP suka halarci wajen.

Bayan kammala wani takaitaccen biki na filin jirgin sama, ayarin motocin Uwargidan shugaban kasar tuni suka nufi kai ziyarar ban girma ga sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Karanta wannan: Mutum 67 aka kashe a Rafah – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Daruruwan mutane ne da suka hada da ‘yan makaranta sun yi jerin gwano a kan tituna domin tarbar uwargidan shugaban kasar a Kano.

Misis Tinubu ta je Kano ne domin kaddamar da wani dakin taro da aka sanya masa suna tsangayar koyar da shari’a ta Jami’ar Maryam Abacha da ke Kano.

Daga cikin shirin da aka baiwa manema labarai a Kano, Uwargidan shugaban kasar da ta kai ziyara za ta bayyana kaddamar da dakin taro na MAUN, tare da tawagarta zuwa gidan gwamnati domin kaddamar da shi, ana sa ran dai za ta tafi Abuja ne da yamma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here