By Aminu bala madobi
Tsohon Ministan noma da albarkatun ƙasa Alhaji Abba Sayyadi Ruma ya rasu a birnin London sakamakon rashin lafiya.
Rahotannin dake iske jaridar solacebase sun nuna cewa, Abba ruma ya je asibitin London ne domin duba lafiyar sa kamar yadda ya sa ba.
Marigayi Abba Ruma ɗan asalin jihar katsina, an haife shi ne a ranar 13 ga watan Maris 1962.
An naɗa marigayin a matsayin Ministan noma yayin mulkin tsohon shugaban ƙasa marigayi Umar Musa yar Adua ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2007.
Haka kuma yabar aiki a matsayin ministan noma a watan Maris ɗin shekarar 2010 lokacin mulkin shugaba Goodluck Jonathan na riƙon ƙwarya.













































