Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya ba da sunan Dakta Bernard Mohammed Doro daga jihar Filato ga majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin sabon minista.
Wannan mataki na zuwa ne domin cike gurbin da ya biyo bayan wasu canje-canjen da aka samu a majalisar ministoci.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa nadin Dakta Doro ya biyo bayan ɗaga likkafar Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, tsohon ministan kula da harkokin jin kai da rage talauci, wanda yanzu yake shugabantar jam’iyyar APC mai mulki.
Kafin aikewa da sunan rahotanni sun nuna cewa shugaban ƙasa ya tattauna da wasu manyan jami’ansa a fadar gwamnati a daren Litinin, inda ya bayyana niyyarsa ta cike wasu kujerun ministoci guda biyu da suka zama fanko a majalisar.
Daga cikin su har da kujerar ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha da aka yi murabus a ‘yan makonnin da suka gabata.
Dakta Bernard Doro, wanda aka haifa a ranar 23 ga watan Janairu, 1969 a ƙauyen Kwall na ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato, ya samu ƙwarewa mai zurfi a fannin kiwon lafiya, gudanar da kamfanonin magunguna da kuma jagoranci a tsawon shekaru fiye da ashirin, a Najeriya da ƙasashen waje.
Ya kammala karatu a fannoni da dama, ciki har da digiri a fannin magunguna, lauya, da digirin digirgir na kasuwancin wanda yayi daidai da fasahar zamani, da kuma digiri na biyu a fannin aikin likitanci na zamani.
Haka kuma, yana daga cikin kwararrun masu bayar da magani kai tsaye a tsarin kiwon lafiya na ƙasar Ingila, inda ya yi aiki a cibiyoyin kula da gaggawa, asibitoci da cibiyoyin lafiya na unguwanni.
Dakta Doro kuma yana taka muhimmiyar rawa a harkokin shiryawa da horar da matasa, tare da gudanar da ayyukan al’umma a cikin Najeriya da wajen ƙasa. Idan majalisar dattawa ta amince da nadinsa, zai shiga cikin majalisar ministocin gwamnatin Tinubu a taron majalisar zartarwa ta ƙasa mai zuwa.












































