Wata Tankar Man fetur dauke da mai a ciki ta fashe a kan hanyar Bida-Agaei a jihar Neja tare da kashe mutane da dama
Hajiya Aishatu Sa’adu, Kwamandan Sashen Hukumar Kiyaye Hanyoyi ta Ƙasa (FRSC), Jihar Neja, ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) cewa har yanzu ba a iya tantance adadin waɗanda suka ji rauni a wannan haɗarin ba.
Ta ce jami’an FRSC sun riga sun fara ayyukan ceto a wurin haɗarin.
Rahotanni sun nuna cewa fashewar ta jawo cunkoson ababen hawa mai tsanani a hanyar, musamman saboda rashin kyawun titin.
Sa’adu ta ƙara da cewa rashin ingancin hanyar ya shafi yadda ake samun rashin saurin kai dauki ga waɗanda suka shiga haɗarin.
Cikakken labarin na nan tafe.
NAN













































