Tinubu ya amince da kamfanonin Jiragen sama 3 a aikin Hajjin 2024

gwamnati, najeriya, hukumomi, kashe kudi,
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta rushe wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnati, yayin da wasu daga ciki kuma za su curesu wuri daya domin rage yawan...

Shugaba Bola Tinubu ya amince da wasu kamfanonin jiragen sama guda uku a matsayin wadanda za su yi jigilar maniyyata aikin hajjin 2024.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya rawaito cewa kamfanonin jiragen su ne Air Peace Ltd. da FlyNas da kuma Max Air.

Karanta wannan: Bayan rahoton da Jaridar Solacebase ta yi an gyara wani asibiti a Jigawa

Mataimakiyar daraktar yada labarai ta hukumar aikin Hajji ta kasa Fatima Sanda-Usara, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a a Abuja.

Fatima Usara ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da wasu kamfanonin jiragen sama guda uku da za su yi jigilar kayan alhazai a aikin Hajjin bana.

A cewarta, kamfanoni ukun sun hada da Cargo Zeal Technologies Ltd. da Nahco Aviance da kuma Qualla Investment Ltd,.

Karanta wannan: Gwamnatin tarayya ta sake yin alkawarin kammala titin Abuja zuwa Kaduna a wannan Shekara

Ta ce amincewar ta biyo bayan kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da maniyatan Najeriya sun yi aikin hajji cikin salama.

Ta bayyana cewa lamarin ya yi daidai da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Najeriya da Saudiyya kan jigilar maniyyatan.

Ta ce hukumar NAHCON za ta yi duk mai yiwu wa, wajen tabbatar da aikin hajjin bana ya tafi yadda ake bukata, tare da mai da hankali kan tsaron mahajjata.

Karanta wannan: Gwamnan jihar Neja ya naɗa sabon shugaban hukumar alhazai

Sanda Usara, tace yanzu haka Ministan harkokin Waje Yusuf Tuggar, na shirin jagorantar wata tawaga daga hukumar NAHCON domin halartar rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin 2024 a ranar 7 ga watan Janairu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here