Tsohon dan kwallon Brazil Mario Zagallo ya mutu

Mario
Mario

Tsohon dan kwallon Brazil Mario Zagallo, ya mutu yana da shekaru 92 a duniya.

Zagallo wanda ya kasance dan wasan gefe, ya lashe kofin duniya har sau biyu na shekarar 1958 da 1962 a jere.

Karanta wannan: Brazil ta haramta sayar da wayoyin iPhone marasa caja

Ya kuma jagorancin tawagar da ya hada ta Brazil mai karfi a duniya da ta kunshi ‘yan wasa irin su Pele da Jairzinho da Carlos Alberto wadanda suka dauki kofin duniya a shekarar 1970.

Zagallo ya kuma sake daukar kofin duniya a matsayin mai horasawa a shekarar 1994.

Karanta wannan: Dan wasan kwallon kafa ya yanke jiki ya fadi, ya mutu

Zagallo ne mutum na farko da ya lashe kofin duniya a matsayin dan wasa da kuma mai horaswa.

Sai wadanda suka bi bayan sa wajen kafa irin wannan tarihi da suka hada da dan wasan Jamus Franz Beckenbauer da na Faransa Didier Deschamps.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here