Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ya baiwa dalibai biyu da suka fi kowa fice a Cibiyar Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina (KSITM) sabbin motoci.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), ya ruwaito cewa an gudanar da bikin mika kyautar ne a ranar Litinin a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Daliban su ne Ibrahim Mai Nasara Bugaje na Sashen Sadarwa da Tsaron Tsarin Kwamfuta, wanda ya kammala da CGPA 4.92, da A’isha Isiaku ta Sashen Injiniyan Kwamfuta, da CGPA 4.75.
NAN ta ruwaito cewa daliban biyu su ne mafiya hazaka a cibiyar.
Wannan kyauta ta cika alkawarin da Radda ya yi a lokacin taron kammala karatun cibiyar a ranar 28 ga Afrilu, inda ya yi alkawarin motoci da aikin dindin mai fansho ga dalibai mafiya hazaka.
Da yake taya masu murnar samun wannan kyautar, gwamnan ya bukace su da su ci gaba da jajircewa wajen cigaban jihar dama kasa baki daya.
“Na taya ku murna da kuka kai ga wannan mataki mai muhimmanci, ina fata ku ci gaba da zama masu amfani ga jihar,” in ji shi.
Radda ya karfafa gwiwar dalibai da su kara kokari domin ci gaban ayyukansu da zama abin koyi ga masu tasowa.
Ya bayyana kyautar a matsayin wani bangare na kudurin gwamnatinsa na tabbatar da aiki tukuru da kwarin gwiwa a karatu tsakanin dalibai a jihar.
“Wannan alkawari ne da aka cika, kuma muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu dama mu yi hakan.
“Muna kuma godiya ga iyaye bisa jagoranci da tallafin da suka bayar, da kuma cibiyar bisa bayar da ingantaccen horo da ilimi,” in ji shi.
Tun da fari dai, Shugaban Ma’aikata, Falalu Bawale, ya ce mika kyautar ya yi daidai da al’adar gwamnati na yaba wa jajorcewa da kara wa dalibai kwarin gwiwa. (NAN)










































