Buhari ya gana da dattawan jihar Katsina

4FAEDB3E 812E 4878 9A16 7200C3AEC596
4FAEDB3E 812E 4878 9A16 7200C3AEC596

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta musamman da wasu daga cikin dattawan jihar Katsinawa a fadar Shugaban kasa dake Villa a Abuja.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya jagoranci tawagar, wanda suka hada da Sanatw Mamman Danmusa da Sanata Abba Ali, sai kuma Alh. Aliyu Mohammed da Alh. Nalado Sarkin Sudan.

A yayin ganawar Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana tare da Shugaban Ma’aikata Farfesa Ibrahim Gambari sai ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire.

Zuwa yanzu dai ba’a samu rahoton abinda aka tattaunawa a yayin zaman ba.

Wannan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da jihar Katsina ke fama da matsalar tsaro na hare-haren yan bindiga da satar mutane.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here