YANZU-YANZU: Burtaniya ta dage takunkumin hana shiga kasar ga ‘yan Najeriya da wasu kasashe 10

DF7098F3 DEF3 4C87 B07E 0DA319DDAEC6
DF7098F3 DEF3 4C87 B07E 0DA319DDAEC6

Gwamnatin Birtaniya ta cire Najeriya da wasu kasashe 10 daga cikin jerin sunayen kasashen da ta sanyawa takunkumim shiga kasar.

Sakataren lafiya na Birtaniya Sajid Javid, ya sanar da hakan a ranar Talata yayin da yake jawabi ga ‘yan majalisar.

Sauran kasashe 10 da aka cirewa takunkumin sun hada da Angola, Botswana, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Namibia, Afirka ta Kudu, Zambia da Zimbabwe.

An sake dawo da jerin jajayen a ƙarshen Nuwamba a matsayin yin taka tsantsan bayan fitowar sabon nau’in Omicron na COVID-19.

A watan Nuwamban da ya gabata ne kasar Birtaniya ta sanar da sanya takunkumi shiga kasar ga wasu kasashe saboda ana ta samun yaduwar sabon na’in cutar Covid-19 mai suna Omicron.
A halin yanzu, duk masu shigowa Birtaniya daga kasashen dole ne su biya kudin sannan su killace kan su na tsawon kwanaki 10 a cikin otal din da gwamnati ta amince da shi

Haka kuma dole ne ayi musu gwajin COVID cikin sa’o’i 48 kafin su tashi zuwa  Birtaniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here