Bamu dauki tubabbun ‘yan Boko Haram aikin soja ba -Rundunar tsaro

9A0EF1EF 149F 4861 8744 1346F2870C42
9A0EF1EF 149F 4861 8744 1346F2870C42

Shugaban hukumar tsaro ta kasa Janar Lucky Irabor ya karyata zargin da ake yi cewa an dauki tubabbun mayakan Boko Haram aikin Soja.

Irabor ya bayyana hakan ne a wajen taron rundunar Operation Safe Corridor wanda ya gudana yau a Abuja.

Ya ce ba’a dauki ko mutum daya cikin mayakan Boko Haram 1,000 da suka kammala zaman gidan gyaran hali aiki ba, yana mai cewa Nigeria ba zata taba yin wannan gangancin ba.

Janar Irabor wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Adeyemi Yekini ya tabbatarwa da ‘yan Nigeria cewa ba za’a taba daukar ‘yan ta’adda aikin soja ba.

Ya ce fiye da ‘yan tada kayar baya 1,000 ne suka kammala zaman gidan gyaran hali tare da gyaran tarbiyya, cikin har da ‘yan kasashen ketare su 16.

Ya kara da cewa yanzu haka fiye da mutane 559 suke daukar horo a cibiyar gyaran hali dake jihar Gombe.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban rundunar Operation Safe Corridor Birgediya Janar Joseph Maina ya ce an fara shirin ne a shekarar 2015 da nufin jan hankalin ‘yan Boko Haram su tuba su mika wuya ga gwamnati.

Ya ce daga shekarar 2016 zuwa yanzu fiye da ‘yan Boko Haram 2,000 ne suka tuba sannan aka mika su gidan gyaran hali suka dauki horo, inda ya bayyana hakan a matsayin wata babban nasara ga shirin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here