Gwamna Yusuf ya nada mataimaka 4 a muhimman mukamai na bada shawara

Governor Abba Kabir Yusuf 640x430 (1)

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada matasa 4 a mukamai na musamman na masu da shawara, a matsayin wani bangare na kokarin karfafa shigar da matasa cikin gwamnati.

Kwamishinan Ruwa, Muhalli da sauyin Yanayi, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata bayan ya mika wa wadanda aka nada takardun nadin a madadin gwamnan.

Sabbin mataimakan da aka nada sun hada da Faisal Musa Wawu Babban Mai Dakko Rahoto a bangaren Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi (SSR), Umar Abdulkadir Koguna Babban Mai Dakko Rahoto kan Kyautata Birni, Aminu Saleh Babban Mai Dakko Rahoto a kan Rumfunan Zabe, Musa Sani Babban Mai Dakko Rahoto kan Tattaro Jama’a.

Yayin mika takardun, Hashim ya ce wannan nadin na nuna kudurin Gwamna Yusuf na baiwa matasa dama su ba da gudunmawa wajen ci gaban Jihar Kano.

“A madadin Mai Girma, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ina farin cikin mika takardun kama ga wadannan matasa domin su ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban Jihar Kano,” in ji shi.

Kwamishinan ya taya wadanda aka nada murna ya kuma bukace su da su gudanar da ayyukansu da gaskiya, mutunci da sadaukarwa ga aikin gwamnati.

Haka kuma ya gode wa gwamna bisa ci gaba da nuna kwarin gwiwa ga matasa da iya taimakawa wajen cimma manufofin ci gaban gwamnatin sa.

“Muna kuma mika godiya ta musamman ga Mai Girma bisa ci gaba da baiwa matasa dama su bayar da tasu gudunmawar wajen gina Jihar aaaaaKano mai kyau,” in ji Hashim.

Ya yi addu’ar Allah ya ba gwamnan lafiya, hikima da ci gaba da samun nasara wajen gudanar da ayyukansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here