Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata a matsayin ranar hutu

images 1 6 684x430

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsayin ranar hutu na kasa don yin bikin Maulidi na bana, wato tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW).

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hutun a madadin Gwamnatin Tarayya cikin wata sanarwa da Sakatariya ta Dindindin a Ma’aikatar, Dr. Magdalene Ajani ta fitar a ranar Juma’a.

Tunji-Ojo ya taya Musulmin Najeriya da na duniya murna kan wannan biki, sannan ya roki ’yan Najeriya da su yi tunani kan dabi’un tausayi, tawali’u da hidimar al’umma da rayuwar Annabi Muhammadu ta ke koyarwa.

“Kowace ranar Maulidi tana ba mu dalilai mu koyi darussa daga rayuwar da ta kasance cike da tausayi, tawali’u da hidimar jama’a.

Wadannan dabi’u ne kasarmu ke bukata a yanzu fiye da kowane lokaci, kuma ina karfafa kowane dan Najeriya, ba ‘yan uwanmu Musulmi maza da mat aba kadai, da su yi koyi da su.” In ji shi.

Ministan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a don samun zaman lafiya da hadin kan kasa, yana mai jaddada cewa kiyaye hadin kai alhakin kowa ne.

Ya roki ’yan kasa da su yi bikin cikin ladabi da girmama juna, sannan ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin Maulidi mai cike da farin ciki da zaman lafiya.

Tunji-Ojo ya jaddada cewa gwamnatin yanzu ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here