PENGASSAN ta dakatar da yajin aikin da ta fara a kasa baki ɗaya

PENGASSAN

Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta dakatar da yajin aikin kasa baki ɗaya da ta fara saboda sabanin da ke tsakaninta da kamfanin matatar mai da sinadarai ta Dangote.

Shugaban PENGASSAN, Comrade Festus Osifo, ne ya sanar da dakatarwar da tsakar ranar Laraba a Abuja, inda ya ce kungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne saboda girmama hukumomin kasa da kuma kokarin sulhu da gwamnatin tarayya ta yi.

Sai dai ma’aikatan sun bayyana rashin jin daɗi da wasu sassa na sanarwar gwamnatin tarayya game da batun, amma sun gargadi cewa za su koma yajin aikin nan take ba tare da wani sanarwa ba idan aka karya yarjejeniyar da aka cimma da kamfanin Dangote.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa tattaunawa tsakanin kungiyar PENGASSAN da kamfanin Dangote da wakilan gwamnati, ta fara ne tun ranar Litinin amma ta tsaya cik bayan shugabancin matatar ya ki amincewa da dawo da ma’aikatan da aka sallama.

Duk da haka, bayan shiga tsakani daga gwamnatin tarayya, an samu matsayar sulhu a safiyar Talata, wanda ya haifar da dakatar da yajin aikin.

Cikakkun bayanai za su zo daga baya…

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here