Gwamnatin Tarayya ta ce kimanin ‘yan Najeriya 2,090 ne suka yi gudun hijira zuwa kasashen Hungary, Poland, Romania, da Slovakia a daidai lokacin da ake ci gaba da yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha.
An tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen tarayya ta fitar, a Abuja.
Babban Sakatare a ma’aikatar, Gabriel Aduda, a cikin sanarwar, ya ce ana sa ran wasu daga cikin ‘yan Najeriya da suka tsere daga Ukraine zuwa makwabtan kasashe za su iso Najeriya ranar Alhamis.
Sanarwar ta kara da cewa “A ci gaba da kokarin da muke yi na kwashe ‘yan Najeriya daga kasashen dake makwabtaka da kasar Ukraine, za mu iya tabbatar da cewa wasu jirage sun tashi a ranar Laraba 2 ga Maris, 2022, domin dauko ‘yan Najeriya a dawo da su gida.
“Ya zuwa yanzu, muna da bayanan da muke da su daga ofisoshin jakadancin Najeriya sun nuna cewa, a kasar Hungary muna da mutane 650, a Poland mutane 350, sai Romania mutane 940, da Slovakia mutane 150.
“Jiragen da za su yi aikin sune, Max Air zai kwaso wanda suke Romania su 560, Air Peace zai taho da wanda suke Poland su 364 da kuma na Hungary su 360.
“Ana sa ran kashin farko na mutanen da aka kwashe za su iso Najeriya ranar Alhamis 3 ga Maris, 2022.
“Muna sake tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa muna aiki ba dare ba rana don ganin an dawo da ‘yan kasar gida gida lafiya.”












































