Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shirya gurfanar da Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, da wasu mutane biyu a gaban kotu bisa zargin almundahanar Naira biliyan daya.
A ranar Litinin ne ake sa ran gurfanar da Farfesa Malumfashi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, tare da Sakataren KANSIEC, Malam Anas Muhammed Mustapha, da Malam Ado Garba, mataimakin darakta a sashen Harkokin kuɗi na hukumar zabe ta jihar.
A cewar ICPC, mutanen uku sun haɗa baki ne a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamba na shekarar 2024 domin yin zamba ta hanyar yin mu’amalar kuɗaɗe da yawa ba bisa ƙa’ida ba, ba tare da la’akari da ƙa’idojin kuɗi da wasu manyan dokokin da suka haramta almundahana da halatta kuɗaɗen haram ba.
SolaceBase ta ruwaito cewa a tuhumar da ICPC ta shigar a gaban kotun, ICPC ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa KANSIEC karkashin Farfesa Malumfashi a watan Nuwamban shekarar 2024 kadai ta miƙa jimillar kudi Naira Biliyan ɗaya da Miliyan Ashirin daga asusun bankin Unity zuwa na SLM Agro Global Farm, wanda ba shi da wata alaka ta kwangila da KANSIEC.
ICPC ta ci gaba da bayyana cewa, a yayin da waɗanda ake ƙara a cikin bayanan da suka bayar na sa kai suka bayyana cewa, an tura wa SLM AgroGlobal kudi ne da nufin tara kudaden da ake buƙata don biyan ma’aikatan zaɓen kananan hukumomi a jihar, kuma kamfanin ya mayar wa KANSIEC duk irin waɗannan kudade da aka yi.
Sai dai bincike ya nuna akasin haka kamar yadda wasikar da wanda ake tuhuma ya aike wa Manajan Bankin Unity da ke Zoo Road a Kano cikakken bayanin inda suka buƙaci a mika musu kudi har miliyan hamsin da tara, Naira Dubu Dari Hudu, tare da cak na kudi daya da kuma jerin sunayen jami’an zaɓe 468 da kuma jerin sunayen jami’an zabe 42 da na taimakan jami’an zaɓe 42.













































