Dalilan rashin ganin Ganduje a ziyarar da Tinubu ya kai Kano

WhatsApp Image 2025 07 19 at 10.34.52 750x430

Lallai babu makawa tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bai halarci ziyarar ta’aziyyar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai Kano a ranar Juma’a ba, sakamakon wata tafiya da ya yi a London, wanda ya fara kwanaki biyar bayan murabus dinsa daga shugabancin jam’iyyar.

SolaceBase ta ruwaito cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Kano ranar Juma’a domin ta’aziyya ga iyalan Dantata bisa rasuwar Alhaji Aminu Dantata, Sai dai kuma ba a ga tsohon shugaban jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ba a yayin ziyarar.

Da yake karin haske game da lamarin, Malam Muhammad Garba, tsohon shugaban ma’aikata na shugaban jam’iyyar APC na kasa, a wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce, saɓanin raɗe-raɗin da kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa cewa Dakta Ganduje ba shi da lafiya ko kuma da gangan aka cire shi daga tawagar shugaban ƙasa, tsohon shugaban na ƙasa ya tafi London ne domin wata ganawa ta sirri da aka shirya.

Garba ya bayyana cewa ziyarar da shugaba Tinubu ya kai, da nufin jajantawa iyalan marigayi hamshaƙin ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, ya sanar da Dakta Ganduje, amma abin takaici, duk da yunƙurin da aka yi na sauya jadawalin jirginsa da tafiyarsa, amma bai samu dawowa gabanin ziyarar ba.

Sai dai duk da kasancewar Dakta Ganduje daga ƙasar waje, kusan kowacce sa’a ɗaya ko biyu ya ci gaba da tattaunawa da jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da kuma shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, domin tabbatar da gudanar da ziyarar shugaban kasar cikin sauki.

Garba ya jaddada cewa murabus ɗin Dakta Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ko kadan ba zai shafi kyakykyawar dangantakarsa da shugaba Tinubu ba da kuma danƙon zumunci da aka gina tsawon shekaru na mutunta juna da kuma daidaita siyasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here