Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin da ya umarci soke rijistar ADC da sauran jam’iyyu 4

Court of Appeal 750x430

Kotun Daukaka Kara dake Abuja ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar na soke rijistar jam’iyyar ADC, Accordda sauran jam’iyyu 3.

Kotun daukaka karar a ranar Talata ta bayyana hukuncin da ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta soke rijistar jam’iyyun a matsayin wanda yake ba bisa ka’ida ba kuma mara tasiri.

Idan za ku iya tunawa, Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya baiwa INEC umarnin ta cire sunan jam’iyyar bisa la’akari da kokarin da ta yi a babban zaben 2023.

Sai dai jam’iyyun siyasa, ciki har da ADC, APP, AA, AP da ZLP, sun nemi a soke hukuncin Babbar Kotun Tarayyar.

Sai dai kotun daukaka kara, yayin da ta bayyana hukuncin a matsayin “wani abu marar tasiri”, ta ce “abinda mai shari’ar kotun farko ya yi ya kai ga wulakanta shari’a ko abinda Kotun Koli ke kira ‘rashin biyayya ga shari’a’.”

Alkalai 3 na kotun daukaka kara da Mai Shari’a Abba Mohammed ke jagoranta, a cikin hukunci na bai daya, ya ce kotun farko ba ta da hurumin sauraron karar tun daga farko.

Kotun daukaka karan ta ce kotun farko ta yi kuskure da ta ci gaba da yin hukunci duk da cewa kotun daukaka kara ta riga ta ba da umarnin a dakatar da sauraron karar, wanda hakan ya hada da fitar da hukunci.

Haka kuma ta ce wanda ya shigar da karar na farko ba shi da hurumin shigar da karar tun asali, don haka ta soke hukuncin kotun farko.

“Hujjojin da ke gaban kotu sun nuna an yi amfani da Sashe na 225A na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima. Hukuncin mai shari’ar kotun farko ya sabawa ka’ida,” in ji kotun daukaka kara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here