Sanata Sunday Karimi ya ce don haka Majalisar Dattawa za ta yi gyare-gyare a kundin tsarin mulki domin tabbatar da cewa gwamnoni suna biyayya ga umarnin kotun koli kan ’yancin kananan hukumomin.
Karin labari: Rundunar sojin Najeriya ta kama riƙaƙƙun ‘yan bindiga a Taraba
Sanatan ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da majalisar za ta gyara a kansu a kundin tsarin mulki akwai kwace ikon gudanar da zaben kananan hukumomi daga hukumomin zaben jihohi a damka a hannun Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).
“Amma wasu gwamnoni za su yaki hakan.
“Shugaba Tinubu ya yi abin da ya dace wajen barin bangaren shari’a ya yi aikinsa, duk kuwa da cewa wa’adin farko na shugaban kasar ke nan ba tare da damuwa da batun sake neman tazarce a 2027 ba,” in ji shi.
Karin labari: Wani malami ya yiwa shugaba Tinubu nasiha kan halin matsin rayuwa
Idan ba’a manta ba, a ranar Alhamis ne Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa sabawa dokar kasa ne rike kason kananan hukumomi na asusun kasa da gwamnatocin jihohi suke yi.
Kotun kolin ta kuma bawa kananan hukumomi cikakken ’yancin gudanar da harkokinsu a hukuncin da ta yanke kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar.
Sanata Karimi ya ce tun shekarar 1999 gwamnoni suka karbewa kananan hukumomi ragama suka mayar da su tamkar wani sashe na gwamnatin jiha, don haka ya ce abin a yabawa shugaba Tinubu ne, kamar yadda jaridar Aminiya ta tabbatar da sahihancin labarin.