Fadar shugaban kasa ta kare matakin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauka na ganawa da iyalan wadanda aka kashe a jihar Plateau a wani zaure da ke kusa da filin jirgin Yakubu Gowon maimakon shiga cikin garin Jos, tana mai cewa takunkumin zirga-zirgar jirage da matsalolin shirye-shirye ne suka haifar da hakan.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana cewa titin saukar jiragen sama na filin jirgin ba ya daukar zirga-zirgar dare saboda rashin kayan taimakon kewayawa, wanda hakan ya sa ba zai yiwu shugaban ya je Rukuba ya dawo filin jirgi kafin duhu ya fadi ba.
Sanarwar ta ce nisan hanya daga filin jirgin zuwa cikin garin Jos kusan mintuna 40 ne, amma rashin damar saukar jirage da daddare ya sa ba zai yiwu shugaban ya shiga gari ya gana da wadanda abin ya shafa sannan ya dawo cikin lokaci ba.
Saboda haka, jami’an gwamnati na jiha da na tarayya sun yanke shawarar kawo wakilan al’ummar da abin ya shafa zuwa wani zaure da ke kusa da filin jirgin domin shugaban kasa ya gana da su cikin gaggawa tare da bin dokokin zirga-zirgar jirage.
Labari mai alaƙa: Harin Jos: Atiku ya soki Tinubu kan ziyarar jaje da ya kai a iya filin jirgi a Plateau
Ziyarar ta biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a yankin Angwan Rukuba na karamar hukumar Jos North a ranar Lahadin, inda aka kashe akalla mutane 28 a daya daga cikin hare-haren da suka fi muni a jihar a ‘yan shekarun baya.
Fadar shugaban kasa ta kuma bayyana dalilin jinkirin tafiyar Tinubu zuwa Jos, tana mai cewa jadawalin aikinsa na ranar Alhamis ya hada da karbar shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Déby Itno a fadar shugaban kasa domin tattaunawar hadin gwiwar tsaro.
Ta ce wannan ganawa ta dauki lokaci fiye da yadda aka tsara, wanda hakan ya jinkirta tashin shugaban zuwa Jos kamar yadda aka tsara.
Sanarwar ta kara da cewa tun farko Tinubu ya shirya zuwa Iperu a jihar Ogun a ranar Alhamis, amma ya soke tafiyar bayan da gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang ya yi masa bayani kan halin tsaro a jihar.
Duk da cewa an gudanar da ziyarar a filin jirgin, fadar shugaban kasa ta ce an cimma burin ziyarar, inda Tinubu ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, ya saurari shugabannin al’umma tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin kawo karshen rikice-rikicen da suka dade suna addabar jihar.
Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai ministan tsaro, babban hafsan rundunar sojojin kasa da kuma sufeto janar na ‘yan sanda, wadanda tuni suka ziyarci yankin Rukuba kafin isowar shugaban.
A yayin ganawar, Tinubu ya sanar da shirin girke sama da kyamarorin sa ido 5,000 masu amfani da fasahar zamani a fadin jihar Plateau, tare da umartar jami’an tsaro su gano masu laifin harin, sannan ya kafa kwamitin tantance asara da biyan diyya.
Haka kuma rundunar sojin Najeriya ta sanar da tura karin sojoji sama da 850 domin karfafa ayyukan tsaro karkashin dakarun Operation Enduring Peace.
Fadar shugaban kasa ta jaddada cewa ziyarar ta kasance mai ma’ana da tsari, kuma manufarta ita ce hada dukkan masu ruwa da tsaki domin magance tushen rikici da rashin tsaro a jihar.
Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya soki ziyarar, yana mai cewa ta nuna rashin tausayi.
Ya bayyana cewa abin takaici ne yadda bayan kashe-kashen da aka yi, ziyarar shugaban ta tsaya ne a filin jirgi ba tare da zuwa wuraren da abin ya faru ko ganin halin da mutanen da abin ya shafa ke ciki ba.
Ya kuma kara da cewa an takaita ziyarar ne domin shugaban ya wuce Lagos domin hutun Easter, wanda hakan na nuna fifita wasu abubuwa a lokacin da kasa ke cikin jimami.













































