Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta umarci ma’aikata a fadin kasa su gudanar da bikin ranar ma’aikata ta 2026 a kan tituna sakamakon rashin aiwatar da dokar mafi karancin albashi ta kasa ta 2024 a wasu jihohi.
Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Emmanuel Ugboaja, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a a Abuja.
Sanarwar mai taken a gudanar da bikin May Day na 2026 a kan tituna idan ba a aiwatar da dokar mafi karancin albashi gaba daya ba a jiharka, ta bayyana cewa matakin ya zama dole sakamakon take dokar da wasu gwamnatocin jihohi ke yi.
Sanarwar ta ce ba za a gudanar da bukukuwan cikin gida ko tarukan liyafa ba a jihohin da ba su aiwatar da sabon albashin gaba daya ba.
Ta ce ma’aikata za su taru a gidajen kungiyar kwadago ko sakatariyoyin kungiyoyi ko filayen jama’a da misalin karfe 7:00 na safe a ranar 1 ga Mayu, 2026.
Daga nan za su fara jerin gwanon lumana a manyan biranen jihohi, wanda zai kare a ofisoshin gwamnatocin jihohi, majalisun dokoki ko ofisoshin shugabannin ma’aikata.
Ta kuma umarci a gabatar da bukatun kungiyoyin kwadago a wuraren da jerin gwanon zai kare.
Kungiyar ta jaddada cewa dokar mafi karancin albashi ta 2024 ta shafi dukkan jihohi kuma dole ne a aiwatar da ita ba tare da wani banbanci ba.
Ugboaja ya gargadi shugabannin kungiyoyin jihohi da cewa duk wanda bai bi wannan umarni ba zai fuskanci hukunci.
Ya ce matakin na da nufin matsa lamba domin a aiwatar da dokar albashi gaba daya da kuma sauran gyare-gyaren da suka shafe ta.
Kungiyar ta bukaci ma’aikata su kasance cikin lumana, hadin kai da kuma tsayawa tsayin daka yayin gudanar da dukkan ayyukan bikin ranar May Day ta 2026.
NAN













































