Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar mutane 11 tare da kone fiye da gidaje 50 a wani rikicin kabilanci da ya faru a ranar Juma’a a garuruwan Akyawa da Udege Kasa na karamar hukumar Nasarawa.
Mai magana da yawun rundunar, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Lafia.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai harin ramuwar gayya sakamakon zargin kashe wasu ‘yan uwansu biyu.
A yayin harin, an kashe mutane 11 yayin da aka kona kimanin gidaje 52 a wadannan garuruwa biyu.
Nansel ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Shetima Mohammed, ya jagoranci tawaga domin duba wuraren da abin ya shafa domin tantance barnar da aka yi tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya.
Ya ce kwamishinan ya nuna alhininsa kan lamarin tare da jajanta wa iyalan wadanda suka rasu da kuma al’ummomin da abin ya shafa, yana mai tabbatar da kudirin rundunar na ganin an yi adalci.
Ya kara da cewa kwamishinan ya bayar da umarnin farautar wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da umartar jami’an bincike da na musamman su tabbatar an gano su, an kama su kuma an gurfanar da su gaban kuliya.
Domin hana sake barkewar rikici, ya ce an kuma tura karin jami’an ‘yan sanda zuwa wuraren da abin ya shafa domin tabbatar da tsaro.
Ya kuma bayyana cewa rundunar na aiki tare da sojoji da kuma jami’an tsaro na NSCDC domin samar da isasshen tsaro da dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Ya kara da cewa an gudanar da taron masu ruwa da tsaki yayin ziyarar inda kwamishinan ya bukaci mazauna yankin su zauna lafiya, su bi doka kuma su hada kai da jami’an tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin taimakawa bincike.
Ya tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa tare da daukar matakan kariya domin hana sake faruwar irin wannan tashin hankali.
NAN













































