Ba zan tsaya takara a zaben 2027 ba – Ortom

Samuel Ortom sabo 750x430

Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ba shi da niyyar tsayawa takara a kowanne matsayi na zabe a babban zaben shekarar 2027.

Ortom ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Terver Akase, ya sanya wa hannu tare da mikawa manema labarai a Makurdi.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawacewa wasu rahotanni a kafofin sada zumunta sun ce Ortom ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar sanatan Benue ta Arewa maso Yamma a 2027.

Ortom ya bayyana cewa babu wata niyya ko kadan da yake da ita na tsayawa takarar kowanne mukami na zabe a shekarar 2027, yana mai cewa ya riga ya bayyana hakan a fili sau da dama.

Ya kara da cewa bai kamata matsayi da ya bayyana a sarari irin wannan ya bukaci wani karin fassara ko kuma wata dabara ta sake bayyanawa ba.

Tsohon gwamnan ya jaddada kudirinsa na ci gaba da mara wa dimokuradiyya baya, da kuma karfafa jam’iyyar PDP tare da bayar da gudunmawa irin ta dattijo, maimakon neman mukamin zabe a 2027.

Ya kuma bukaci jama’a su dauki rahotannin da ke yawo a matsayin kirkirarre maras tushe.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here