Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci biyu daga jihohin Filato da Enugu, wato Dakta Bernard Doro da kuma Dakta Kingsley Udeh.
Bikin rantsuwar ya gudana ne a dakin taron majalisar zartarwa da ke fadar gwamnati a Abuja, kuma kafin fara zaman majalisar zartarwa ta tarayya da dukkan mambobinta suka halarta.
Shugaba Tinubu ya shawarci sababbin ministocin da su yi amfani da ƙwarewar da suka samu wajen gudanar da ayyukansu, tare da mai da hankali kan nagarta da ingantaccen aiwatar da ayyuka.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayar da rahoton cewa Dakta Doro, wanda masanin magunguna ne kuma lauya, ya maye gurbin Farfesa Nentawe Yilwatda, tsohon ministan kula da harkokin jin kai da rage talauci, wanda yanzu shi ne shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa.
Haka kuma Dakta Udeh ya cike gurbin da tsohon ministan kimiyya, kirkire-kirkire da fasaha, Uche Nnaji, ya bari bayan ya yi murabus saboda cece-kuce da aka samu dangane da takardun karatunsa.
Dakta Udeh ya taɓa riƙe mukamin babban lauyan jihar Enugu da kuma kwamishinan shari’a kafin wannan naɗin.
Majalisar dattawa ta riga ta tantance kuma ta amince da nadin sababbin ministocin, sai dai har zuwa lokacin da kammala rahoton nan, ba a bayyana mukaman da za su riƙa ba.












































